Gwamnan Jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tafi zuwa Amurka domin halartar wani taro na tsawon mako guda a Harvard.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaru Muhammad Garba ya fitar, inda yace Ganduje zai halarci taro ne akan ” shirin cigaban shugabanci” a Makarantar Kasuwanci ta Harvard, Boston.
KARANTA WANNAN LABARIN: An ceto mabiya cocin Celestial guda 3 da akayi garkuwa dasu a Ogun
Yace Gwamnan ya miƙa ragamar mulki, tare da bada cikakken iko ga Mataimakin sa Nasir Gawuna, domin ya yi aiki a Matsayin Gwamna a Jahar.
Sanarwar ta ƙara dacewa, duk wasu hada-hada a kaishi a ofishin Mataimakin Gwamnan domin gudanar da aikin da ya kamata.