Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya taya masarautar kasar Saudiyya murnar cika shekaru casa’in da biyu da dunkulewa a matsayin masarauta.
Ganduje Ya bayyana haka ne wajen taron bikin murnar hadewar masarautar da ya gudana a dakin taro na The Afficent dake jihar Kano, wanda ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya dake jihar nan ya shirya a yau Asabar.
KARANTA ANAN: APC Ta Bayyana Sunan Sanatan PDP, A Cikin Sunayen Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu
Gwamna Ganduje ya yabawa mahukuntan Sadiyya bisa irin gudunmawar da suke baiwa duniyar musulunci da musulmi, musamman wajen bayar da gurbin karatu da kuma daukar dawainiyar daliban da suka fito daga sassan kasar nan.
A nasa jawabin jakadan kasar ta Saudiyya Khalil Ahmad Al-Adamawi ya bayyana cewa akwai dadaddiyar alaka tsakanin Najeriya da Saudiyya ta fuskoki da dama ta fuskar ilimi da addini.
A karshe Khalil Ahmad yayi fatan dorewar fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kaduna ta nuna damuwa kan cinkoson ababan hawa daga Kaduna zuwa Abuja
Gwamnatin Kaduna ta nuna damuwarta kan yadda matafiya ke fuskantar dogon cunkoson ababen hawa a Titin Kaduna-Abuja a ‘yan kwanakin nan.
Kwamishin tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata Sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna.