Gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ware naira biliyan 45.6 ga bangaren ilimi a kasafin kudin 2021. Kasafin kudin na 2021 da aka yi take da ‘Budget for Economic Recovery and Sustainable Development’ ma’ana kasafin kudin farfado da tattalin arziki da ci gaba mai dorewa.
Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Alhaji Nura Dankadai, ne ya tabbatar da hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar alhamis A Kano.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Ganduje ya bai wa bangaren ilimi muhimmancin gaske wajen ganin an kawo wa al’umma ci gaba. Inda ya ce wannan dalilin ne ma ya sanya aka ware wadannan makudan kudaden wanda ya dauki kashi 25.68 na kasafin kudin 2021.