Hukumar gudanar wa ta gidan Radiyon Nagarta dake Jihar Kaduna ta karrama Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, da lambobin yabo guda biyu.
An gudanar da taron karramawar ce, a harabar gidan Rediyon dake Jihar Kaduna.
A yayin da gidan Rediyon ya ke bikin cika shakaru goma sha biyar da fara gabatar da shiryen su, sun karrama Gwamnan da lambar yabo mai taken “Tauraron Siyasar Arewa” da kuma wata labar girma mai taken “Barden Hausa”.
An karrama Gwamnan ne, jim kadan bayan ya kammala hira ta awa daya a gidan Rediyon, inda ya tattauna muhimman batutuwa, wandanda su ka shafi Gwamnatin sa, tsawon shekaru shida.
KARANTA WANNAN LABARIN: Chelsea na zawarcin Lukaku na Inter Milan
A jawabin sa, Shugaban hukumar gidan Rediyon Nagarta, Malam Abdulkareem Ali, ya bayyana dalilin karrama Gwamna ganduje, bisa duba da yadda ya rike Jihar Kano, da aiwatar da ayyukan more rayuwa da tabbatar da tsaro, da kuma yadda ya ke tafiyar da harkokin siyasar sa cikin hikima, da nuna kwarewa.
A jawabin Mai Girma Gwamnan, ya yaba wa hukumar gunawar gidan Rediyon, bisa yadda su ke gabatar da shiryen-shiryen su da yadda su ke kokarin hada kan al’umma, da kuma yadda su ka duba chanchanta, su ka bashi kyautukan ban girma har guda biyu a lokaci guda, inda ya bayyana kyautar a matsayin kyautar al’ummar Jihar Kano baki daya.