Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin binciken aikin hanyoyi masu tsawon kilomita biya-biyar a faɗin ƙananan hukumomin 44 dake jihar.
Ayyukan da tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayar da su, a lokacin gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje na mataimakin gwamna kuma shi ne kwamishinan ƙananan hukumomin jihar a wancan lokaci.
Da ya ke ƙarin haske a kan kafa kwamitin binciken, kwamishinan yaɗaabarai na jihar, Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin ne domin yin duba a kan ayyukan, kuma ba za ta yi wata-wata ba wajen soke duk kwangilar da aka gano cuwacuwa a cikinta.
Kwamishinan ya ce kawamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin babban sakataren Ma’aikatar Ayyuka da kuma wakilai daga hukumar tsara irane ta jihar (KNUPDA) da Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi a matsayin ‘yan kwamiti.
Malam Muhammad ya ce kwamitin zai gano matsayin aiwatar da kwangilolin da kuma adadin kuɗaɗen da aka biya ’yan kwangilar.
A nasa ɓangaren kuwa, tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso wanda shi ne ya bayar da ayyukan tun da farko ya yi na’am da matakin.
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan, wanda kuma yanzu yake zama a matsayin kakakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam ya ce sun yi maraba da matakin kuma sun daɗe sun jiran hakan.
“Abin sha’awar shi ne Gwamna Ganduje, a lokacin yana Mataimakin Gwamna shi ne Babban Mai Kula da aikin a faɗin jiha”, inji Aminu.
Gwamnatin Kwankwaso ce dai ta bayar da aikin a ƙananan hukumomi 44 na jihar kafin daga bisani a yi watsi da su bayan saukarta daga mulki.