• Dukkannin dabiban da suka fito daga kananan hukumomin jihar ne, za su amfana da wannan tsarin.
• Ganduje ya Umarci kananan hukumomin jihar da su kafa kwamitin da zasu zakulo yaran da zasuci wannan moriya.
• Yaran marasa galihu ne zasu ci gajiyar wannan shirin.
Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Gwamnatin Jahar Kano ta umurci Kananan hukumomi 44 dake Jihar, dasu biya kudin Jarabawar NECO ga Dalibai Dubu 10, 400 Yan asalin Jihar.
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Sule Garo ne ya bayyana haka, ta bakin Jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Farouq Ghali Masanawa, a cikin sanarwar daya fitar a yau Lahadi.
Sule-Garo ya kara da cewa, Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umarnin biyan kudaden jarabawa ga Dalibai marassa galihu guda dari 400 a kowacce Karamar hukuma na cikin birni jihar.
Kananan hukumomin sun hada da; Kano Muncipal, Dala, Nasarawa, Gwale, Tarauni, Ungogo, Fagge da kuma karamar hukumar Kumbotso.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu ba sai an sha wahala ba ake yin suna a harkar fim
Sule Garo ya kara da cewa kowacce Karamar hukuma zata dauki nauyin biyan kudaden jarabawa ga Dalibai marassa karfi guda 200 da suka fito daga yankin ta.
A cewar sa, Gwamnati ta umarci Kananan hukumomi 44, dasu nada kwamitoci domin zakulo wadannan Daliban da suka dace.
Kwamishinan ya kuma bukaci masu hannu da shuni, da kungiyoyin da kai, da su hada hannu da gwamnatin jihar, domin farfado da martabar ilmi a fadin jihar baki daya.
Comments 1