Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace gwamnatin sa zata ci gaba da taimakon masu sana’ar shirya fina-finan Hausa da nufin daga likafar sana’ar zuwa babban mataki.
Gwamnan na wannan jawabi ne yayin da sabbin shugabannin kungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN) ta kai masa ziyara a ofishinsa a yammacin yau juma’a karkashin jagorancin sabon shugabanta Ado Ahmad Gidan Dabino.
Gwamna Ganduje yace gwamnatin sa zata samo guraben horaswa ga mambobin kungiyar a kasashen ketare da nufín inganta sana’ar shirya fim wadda a cewar sa mutane da dama ke kallon ta a kaskance sakamakon rashin samun horo da wadanda suka tsinci kansu a ciki basa yi.
KARANTA ANAN: Putin Ya Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hade Yankunan Ukraine
Ya kara da cewa gwamnatin kano zata duba yiwuwar samar da makarantar koyar da sana’ar shirya fim da kuma sauran sana’oin da ke da jibi da ita domin taimakon wadanda ke ciki da kuma samar da ayyukanyi ga dumbin matasan jihar nan,inda ya hore su da guji siyasantar da al’amuran kungiyar.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar ta MOPPAN Ado Ahmad gidan Dabino yace makasudin ziyarar tasu shine gabatar da sabbin shugabannin ta da kuma rokon gwamnati da ta kara shiga cikin lamarin su ta hanyar sama musu ababen hawa domin rage dawainiya yana mai jaddada irin alakar da take tsakánin gwamnati da kuma masana’antar fim ta kano la’akari da yadda take jan ‘ya’yan kungiyar a jiki
Ziyarar ta yau ta kunshi shugaban hukumar tace fina_finai da dab’i ta jihar nan Isma’il Afakallah da sauran sabbi da tsoffin mambobin kungiyar masu shirya fim a anan Kano.
A wani labarin kuma: Jigon APC: Tinubu ya tafi Landan ne saboda ba za su bar shi ya huta ba a Legas, Abuja
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi Landan ne domin ya huta, kamar yadda mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo, ya bayyana.
Rashin halartar Tinubu a wajen taron yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi a ranar Alhamis din nan ya janyo ce-ce-ku-ce, inda aka rika yada jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ba shi da lafiya.