Gwamnatin jihar Legas ta samar da wasu hanyoyi gabanin babban taron gangamin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi ranar Talata a jihar.
A wata sanarwa da babban Manajan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas, Bolaji Areagba, ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, gwamnatin ta ce hanyoyin da za a bi za su rage wahalhalu a lokacin tafiye-tafiye kafin da kuma lokacin taron.
KARANTA HAKANAN APC Ta Musanta Batun Tinubu Zai Mayar Da Legas Birnin Tarayya
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa LASTMA ta shawarci masu ababen hawa daga filin jirgin saman yankin zuwa Maryland da su yi amfani da Kodesoh ta Obafemi Awolowo don isa Kudirat Abiola ta Ojota da kuma hada da wuraren da suke zuwa.
Hukumar ta ce, “Yayin da jerin gwanon ke kan babbar hanyar mota a kan titin Ikorodu, ayyukan titin zai kasance don amfani da masu ababen hawa ba tare da wata matsala ba.
Har ila yau, ta shawarci masu ababen hawa daga filin jirgin saman yankin zuwa Ketu-Mile 12 da su bi hanyar Kodesoh ta hanyar Obafemi Awolowo Way ta hanyar Sakatariyar Titin Mobolaji Johnson Avenue ta hanyar Ojota Interchange zuwa Ketu, su kuma hada da wuraren da suke zuwa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa A wani bangaren sanarwar ta kara da cewa, “domin a rage wahalhalu, a lokacin tafiya, da kuma tabbatar da tsaro da kare duk masu amfani da hanyar, za a baza jami’an tsaro isassu a dukkan hanyoyin da aka kebe zuwa filin wasa da sauran hanyoyin.
“Muna neman goyon baya da hadin kan duk masu amfani da hanyar tare da neman afuwar duk wata matsala da hakan ka iya haifar.”
A Wani Labarin Kuma Manufofin Kuɗi Na Iya Rage Hauhawar Farashin A Cikin Dogon Lokaci — Masanin Tattalin Arziki
Wani masanin tattalin arziki, Dokta Ayo Anthony ya ce sabuwar manufar kudi da Gwamnatin Tarayya ta yi na iya taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya cikin dogon lokaci.
Anthony ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Abuja.