Gargadi: Ku sani Najeriya ba bola bane, FG ga masu shigo da kayayyaki
Babu wani guri ga Yan kasa masu shigo da kayayyaki da mataimakansu wa’inda ke kokarin maida kasar mu tamkar bola akan wasu kayayyaki marasa muhimmanci. Inji Ministan Kasuwanci da Kanfanoni, Otunba Niyi Adebayo.
KARANTA:-Rahoto: Cikin wata bakwai, an yi garkuwa da ɗalibai 1,065, an kashe 6
Adebayo ya bayyana hakane a wajan kaddamar da hukumar dake tantance ingantattun kayayyaki a wani ofishinta na Jahar Ekiti ranar Lahadi.
Yace kundin tsarin Hukumar na 2015 ya basu damar kama duk wanda ya saba doka sannan ta hukunta shi.
Hukumar SON zatai hukuncin ga masu keta doka, sannan a shirye hukumar take don aiki da daidai ko jama’a masu son inganta Al’umma da kuma wannan Kasa.
Adebayo yace Gwamnatin tarayya zata gina dakin gwaje-gwajen kayayyaki don tantance ingantattun kaya.
Gwamna Fayemi Kayode yace wannan ofishin zai taimaka wajan tattalin arziqi da habbaka kasuwanci a jahar.
Yace zamu cigaba da samar da ingantattun kayayyaki sannan mu hada guiwa da hukumar SON don bin doka.
Yace Ina mai tabbatar ma Jagoran hukumar ta SON zamu sanya kofin su na yin titi abu na farko da damuyi nan gaba.
Comments 1