Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da dagacin ƙauyen Mashio da ke ƙaramar hukumar Fune ta Jihar Yobe.
A daren Lahadi ne ne maharan da suka razana mazauna da harbe-harbe suka ɗauke Alhaji Isa Mai Buba Mashio da ɗansa mai shekara 35.
Wani wanda ya ganewa idonsa, ya ce daga baya ɗan basaraken ya tsere amma ya samu raunin bindiga.
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai Wakiltar Mazabar Jajere, Chrioma Buba Mashio ya ce jama’a sun ɗauka harin Boko Haram ne, kafin daga baya suka fahimci cewa masu garkuwa da mutane ne.
Ya ce ’yan banga da jami’an tsaro na bin sawun maharan tun ranar Asabar da dare.
“Yanzu haka muna cikin daji tare da jami’an tsaro da mafarauta muna bin sawunsu. Muna zargin a ƙafa ta suke tafiya domin babu alamar sawun mota, kawo yanzu”, kamar yadda ya bayyanawa manema labarai.
Ɗan majalisar ya ce maharan sun kira waya suna barazanar kashe basaraken idan ba a daina bin su ba “amma mun yi watsi da su”.
Ya ce yana tuntuɓar manyan jami’an gwamnati domin ganin an ceto basaraken daga hannun ’yan bindigar.