By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Abia, a ranar Juma’a, ta dakatar da yajin aikin masana’antu da suka fara, kan abokin aikinsu da aka yi garkuwa da shi Farfesa Uwadinachi Iweha.
Wannan kudiri ya zo ne bayan wani taron gaggawa na kwamitin jami’an jihar domin duba kokarin da gwamnatin jihar Abia da hukumomin tsaro suka yi na ceto Iweha.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsaro: Osinbajo Yayi Kira Ga Amurka Dasu Kara Hada Kai A Yakin Da Suke Da ‘Yan Ta’add
An yi garkuwa da Iweha ne a ranar 6 ga watan Yuni kuma a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, likitocin suka shiga yajin aikin.
A cewar likitocin, “Bayan yin x-ray ga dukkan lamarin kamar yadda gwamnati da hukumomin tsaro suka gabatar,” SOC ta yanke shawarar “an fara aiki a dukkan cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da na gwamnatin jihar Abia da karfe 10:00 na safe ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni 2022.”
A wani labarin kuma Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Asiwaju Tinubu ya mika Fom din sa na son tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC ga hukumar zabe ta INEC.
Tinubu dai shine yayi nasarar zama ɗan takarar jam’iyyar, bayan nasarar da ya samu a zaben fidda gwani daka gudanar a Abuja tsakaninsa da yan takara 14.
Jagoran jam’iyyar dai tun a ranar Laraba ya saka hannu kan Fom din takarar, tare da mika shi ga hukumar kwanaki biyu kafin wa’adin da INEC ta basu ya kare.
Wannan batu dai mai taimakawa Tinubun kan kafafen yada labarai Tunde Rahman ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.
To sai dan kan hakan mun sake tuntubar Tunde Rahman Amma yace bashi da cewa yanzu, amma a kira ce shi.
Daga cikin sunayen da Tinubun ya bayar domin zabar daya cikin su har da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari.
Yanzu haka dai Masari na kan gaba cikin wadanda ake tunanin Tinubun zai dauka matsayin mataimaki.