• An saki sarkin ne a yau, wanda aka yi garkuwa da shi tun ranar Talatar da ta gabata.
• Wasu rahotanni na cewa, sai da aka biya naira milliyan biyu kafin sakin sarkin da matar shi.
• Shugaban karamar hukumar Ido ya tabbatar da sakin mutun biyun.
Masu Garkuwa da mutane, sun saki sarkin yankin Araromi Idowu, na karamar hukumar Ido a jihar Oyo Mai suna Baale Tafa Apapan da matar shi.
An dai yi garkuwa da mutanan biyu ne, a gidan su, da sanyin safiyar ranar Talatar da ta gabata.
Wasu rahotanni da ba tabbatar ba, sun ce kafin sakin sarkin da matar shi sai da ka biya kudin fansan da ya kai naira milliyan biyu..
Sai dai a yunkirin da akayi na tabbatar da sakin mutane biyun, ta bandmgaren Mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Oyo, abun ya citira
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari zai tafi birnin Landan
Sai dai Shugaban karamar hukumar Ido Mr Sheriff Adeojo ya tabbatar da sakin basaraken da kuma matar shi.