Ministan wasanni na ƙasar Najeriya wato Sunday Dare ya bayyana cewar gasar guje-guje da tsalle-tsalle da za a yi a jahar Edo tananan daram babu gugu babu ja da baya, kamar yadda wasu suke raɗeraɗin cewar za a dakatar da gasar.
A jiya dai akaji wasu na yaɗa labaran ƙanzon kurege game da gasar daza’a gudanar a jahar ta Edo wato gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta shekarar 2020 cewar baza a gudanar da wannan gasar ba sakamakon rikicin zanga-zanga da akeyi a wasu sassan jahohin na ƙasar ta Najeriya.
An dakatar da gasar ne a lokacin da cutar nan ta Coronavirus tayi tsamari inda tun a watan Afrilu aka dakatar da harkokin wasanni a Najeriya, sai dai a makon daya gabata ne dai aka bayar da sanarwar ɗage takunkumin da aka sanya na hana harkokin wasanni a Najeriya inda yanzu za a dawo fagen fama.
Daga ƙarshe ministan wasannin wato Sunday Dare ya bayyana cewar suna nan suna jiran shawarwari daga masana lafiya ta yadda za a gudanar da wannan gasa ta guje-guje da tsalle-tsalle a jahar ta Edo.