Dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ba zai buga muhimmin wasan da za su yi da Dynamo Kiev a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata ba, saboda raunin da ya ji a kafarsa, in ji kulob din a yau Lahadi.
“Gwajin da aka yi a safiyar yau ya tabbatar da cewa dan wasan Gerard Pique yaji rauni akafarsa ta dama, kuma zai yi jinya” in ji kulob din a shafin yanar gizon su.
Sanarwar ba ta bayyana tsawon lokacin da ake sa ran Pique zai yi jinya ba.
Amma Pique ya ji rauni ne a minti na 70 a ranar Asabar, yayin da Barcelona ta tashi kunnen doki 1-1 a gida da Alaves a gasar La Liga a wasan farko da kungiyar ta yi tun bayan korar kocinta Ronald Koeman. An maye gurbinsa da Clement Lenglet. Wanda bayan tashi wasan Barcelona ta ci gaba da zama a matsayi na tara a teburi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Anyi Jana’izar Tsohon Minista Abba Ruma
Barcelona ce ta uku a gasar cin kofin zakarun Turai a rukunin E, bayan da ta sha kashi a wasanninta biyu, na farko da Tasha kashi 3-0 a hannun Bayern Munich da Benfica, sannan ta doke Kiev da ci 1-0, Pique ya ci kwallon a filin wasa na Camp Nou.
Yanzu haka Barcelona ta na da maki ukune kacal a Rukunin.