• Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, ya bayyana yadda kyawawan halayen shugaba Buhari suka jawo hankalinsa
• Gwamnan yace adalcin shugaba Buhari, kirkinsa da saukin kan da yake da shi ne suka sanya ya sauya sheka zuwa APC
• Farfesa Ayade ya ce Buhari ya amince da kawo ziyara jihar Cross River, kuma zai kaddamar da ayyuka yayin ziyarar.
Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya bayyana cewa, adalci da saukin kan shugaba Muhammadu Buhari su ka janyo hankalin shi ya koma Jam’iyar APC Mai mulki.
Gwamna Ayade, Wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC kwana kin baya, ya yi wannan jawabi ne a garin Daura dake jihar Katsina.
Ayade na ɗaya daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC guda 12 da suka kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyarar barka da sallah a mahaifarsa.
“Adalcin Shugaba Buhari da saukin kansa ya sa na sauya sheka zuwa APC” inji Gwamna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kubutar da Fasinjoji goma sha daya da akayi garkuwa da su a Zamfara
Gwamnan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Buhari yana rayuwa ne fiye da tunanin mutane.
Kazalika gwamnan ya cigaba da cewa, “Shugaba Buhari ne ya jawo hankalina zuwa jam’iyar APC ta hanyar saukin kansa, kirki, da adalci, halayen da ba’a cika samunsu a cikin mutane ba sai kaɗan.”
A karshe Gwamnan ya ce tuni Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ya ziyarci jihar ta Cross Rivers domin ya kaddamar da wasu aiyukan a watan Satumba shekarar nan.
Comments 1