Kotun koli ta Nijeriya bisa yanke hukuncin da tayi Akan zaben jihar zamfara wanda ya baiwa jam’iyarsa ta PDP nasara.
Dan takarar shugabancin Nijeriya karkashen jam’iyar PDP Atiku Abubakar yace Kotun koli ta tabbatar da adalci, biyo bayan hukuncin da ta yanke wanda ya baiwa Bello matawalle damar kasancewa sabon gwamnan jihar Zamfara.
Babu abinda ya fi dadi a kunnuwan masu imani kamar Jin wannan hukuncin adalcin da Kotun ta yanke cikin watan Ramadan mai Alfarma” kamar yadda Atikun ya fadi ta hanyar hadimin sa Mr Paul Ibe.
Atiku ya yabawa alkalan da suka yanke wannan hukuncin, bisa namijin kokarin ganin cewan ba’a tauye gaskiya ba ko kadan, saboda sun dubi kudurin yan Nijeriya dama kasar baki daya.
Allah ya kasance farko, sannan kasar mu Nijeriya, haka ya kamata ace duk wani dan Nijeriya mai nagarta ya kasance.
Bayan da gaskiya ta bayyana, jama’a sun cika da farin ciki, yayin da kowa ke Sam barka da aukuwar wannan alamarin kamar ya fadi.
A karshe ya taya sabon gwamnan murnar samun wannan nasarar tare da illahirin jama’ar jihar zamfara wandanda a yanzu suka samu gwamnan da zai share musu kukan su.