• Babu batun daukar Sabin jami’ai a yanzu a hukumar kare haddura ta kasa.
• Labaran da ake yada wa na daukan sabbin jami’ai a hukumar karya ne.
•Jamin wayar da kan jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan a Abuja.
Hukumar kare haddura ta kasa FRSC ta ja hankalin masu ne man shiga hukumar, da su kauce wa yan damfara, da ke cewa hukumar za ta debi sabbin jami’ai.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a na hukumar Bisi Kazeem ya fitar a yau Alhamis, a babban birnin tarayya Abuja.
Kazeem ya ce, ya zama wajibi, a wayar da kan jama’a domin kauce wa yan damfara, daga yaudaran masu ne man aikin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalejin Nuhu Bamalli ta tsawaita jadawalin Karatun ta
Ya ce, an ja hankalin hukumar dangane da wani rubutu da aka wallafa na yaudara, inda ake cewa hukumar ta fitar da sunayen wadanda zata ba aiki.
Don haka hukumar na sanar da al’uma cewa, a yanzu ba ta diban sabbin jami’ai, kuma bata wallafa sunan kowa ba, a shafukan su na yanar gizo.
Kazalika hukumar ta ce, tsare-tsaren daukan sabbin jami’ai ta, ta kan yishi ne a bayya ne. Kuma su kanyi hakan ne, ta hanyar tallace-tallace, da wayar da kan al’uma ta kafafen yada labarai.
“Kuma sanarwar kanzo ta cikin shafin yanar gizon hukumar, na www.frsc.gov.ng, da shafukan sada zumunta, da kuma gidan radiyon hukumar da ke yada shirye shirye akan mita 107.1 FM”. Inji shi.
A karshe ya shawar I al’uma Baki daya, da su nisanta kansu da duk wasu bayanan karya da wasu ke a lakantawa hukumar domin kauce wa shiga komar yan damf
Comments 1