Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi bakunci wasu daga cikin tawagar tsohuwar gwamnatinsa.
Tawagar bisa jagoranci Dr Nasiru Yusuf Gawuna, sun ziyarci Gwamnan me, wanda yanzu haka ke gidansa na Abuja.
KU KARANTA: Kano: Kungiyar NULGE Ta Nemi Hadin Kan Gwamnan Kano Domin Aiki Tare
Wannan dai itace ziyara ta farko da gwamnan ya damu, tun bayan daya bar Mulkin jihar.
Daga cikin yan tawagar akwai tsohon Kwamishinan komai da ruwan ka Muntari Ishaq Yakasai da sauran su.
Shugaban karamar hukumar birni Fa’izu Alfindiki ne ya sanar da hakan, a shafinsa na Facebook tare da wallafa hotunan su yayin ziyarar.
A wani labarin kuma: Kungiyar Kwadago Ta Nemi Hadin Kan ASUU Domin Tsunduma Yajin Aiki
Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta rubutawa dukkanin kungiyoyin ta 43 da suka hada kai domin tsunduma yajin aiki da aka tsara za a fara a ranar Laraba 7 ga watan Yuni, 2023, inji rahoton The PUNCH.
Yajin aikin ya biyo bayan karin farashin litar man fetur, da gwamnatin tarayya tayi.
Wasu daga cikin kungiyoyin NLC sun hada da – Kungiyar Malaman Jami’o’i, Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Kasa, Kungiyar Malamai ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan Shari’a ta Najeriya, Kungiyar Ma’aikatan jinya ta Kasa da Ungozoma da dai sauransu.