Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce ‘yan Nigeria a yanzu sun fahimci kuskuren da suka tafka na zabar jam’iyya mai mulki ta APC, kuskuren da ya zama wajibi a garesu su gyara shi a zaben 2023 ta hanyar zaben jam’iyyar PDP.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a Yola, babban birnin jihar Adamawa a inda ya kai ziyarar duba aikin babbar gadar sama da kuma titunan kasa da gwamnan jihar Adamawa ya gidana, Ahmadu Fintiri.
Wike ya ce gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta kasa dakile cin hanci da rashawa, da kuma gaza kawo karshen matsalar tsaro, tare da haddasa rikici na bambance bambance da suka hada da kabilanci da na addini.
A cewar sa, ayyukan da gwamnonin jam’iyyar PDP suka aiwata, a cikin wannan yanayin na tabarbarewar tattalin arzikin kasa sakamakon bullar annobar COVID-19, ya nuna jajircewarsu kan son ci gaban kasar da kuma bunkasa rayuwar ‘yan Nigeria.