Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yace takwaransa na Jam’iyyar PDP Gwamna Obaseki na jihar Edo ya gaza.
Ganduje wanda shi ne shugaban kwamitin yaƙin zaɓen da za a yi a jihar Edo ya ce gazawar Obaseki wata babbar dama ce da jam’iyyar APC wajen lashe zaɓen da za a yi.
Ganduje da Obaseki sun kasance ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya kafin takwaran nasa na jihar Edo ya koma jam’iyyar PDP biyo bayan rashin nasarar samun tikitin tsayawa takara.
Yanzu haka dai Fasto Ize-Iyamu shi ne zai takara a jam’iyyar APC shi kuma Obaseki ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP.
“Obaseki zai zamowa PDP alaƙaƙai saboda babu wani abin muzo mu gani da yiwa jihar Edo” cewar Ganduje.
“Ina faɗa muku ya gaza, kuma hakan babbar dama ce a gare mu, zamu kara da shi”.
Kwamitin da shugaban kasa ya tura jihar suna can domin tallafawa ɗan takarar jam’iyyar APC ɗin Fasto Ize-Iyamu domin ganin ya kai ga gaci.