By Abbas Yakubu Yaura
Kakakin Majalisar Wakilai ya yi kira da afara kamawa tare da gurfanar da ma’aikatan lafiya dake bada satifiket na bogi na cutar COVID-19.
Kiran na sa ya biyo bayan sanarwar da Darakta Janar na Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dr. Ifedayo Adetifa, ya yi, cewa an kama wasu mutanen da suka aikata wannan haramtacciyar hanya tare da mika su ga hukumar tsaro ta, DSS, bisa tuhumar da ake yi musu.
Adetifa, wanda ya bayyana hakan a yayin zaman tattaunawa na kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama tare da shugabannin hukumomi da na ma’aikatar sufurin jiragen sama na tarayya, yace wasu masu cin hanci da rashawa sun hada baki da wasu jami’ai a filin jirgin domin aikata laifukan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hakan yasa kakakin majalisar ya bada shawarar kafa wata hukuma ta gwamnati, kamar hukumar kula da harkokin sufuri, TSA, da zata tsara ayyukan masu aiki a cikin filayen jiragen sama a Najeriya.
Kazalika yace, “Ba zai kasance daya daga cikin irin wadannan zaman da ba za a samu sakamako ba, ina ganin daya daga cikin sakamakon da za a yi shi ne yin dokar data kafa wata hukuma ta musamman da zata rika kula da ayyukan filayen jiragen sama kamar TSA.
Da yake amsa tambayoyin da shugaban kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama na majalisar Nnolim Nnaji ya yi kan zargin cin hanci da rashawa da jami’an hukumar ke yi a filayen tashi da saukar jiragen sama, Manajan Daraktan FAAN, Rabiu Yadudu, yace ana gudanar da taruka akai-akai tsakanin jami’an hukumar da ma’aikatan a duk mako, don ilmantarwa da bincika ayyukansu.