Ghana dai ta fice daga gasar cin kofin Afrika ta 2021 a matakin rukuni.
Wannan ya biyo bayan kayen da ta sha a hannun Comoros da ci 3-2 a daren Talata.
Tawagar ta Black Stars sun zo wasansu na karshe a rukunin C da maki daya kuma suna bukatar nasara don samun ci gaba, Wanda a karshen wasan abun ya gagare su.
Toh sai dai tun a Mintina na 25 ne Andre Ayew ya Samu Jan kati Wanda hakan ya Sanya Kasar Ghanan karkarewa wasan da Yan wasa 10.
Duk da Ghana ta yi Yunkurin farfadowa a wasan Amma amintina na 85 Ahmed Mogni ya ci wa Kasarsa ta Comoros kwallo na 3 Wanda hakan yasa Gana ta fice daga gasar Kai tsaye.