Kungiyar masu gidajen kallo na Cinema, ta kasa ta ce ta samu Naira miliyan 378 daga tikitin da aka sayar a fadin kasar nan a watan Agusta.
Shugaban kungiyar ta CEAN na kasa, Mista Ope Ajayi, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ajayi ya ce adadin ya nuna karuwar kashi 28 cikin dari idan aka kwatanta da Naira miliyan 294 da aka samu a watan Agustan 2021.
KARANTA ANAN; Katsina: Ruwan Sama Mai Ƙanƙara Ya Lalata Gonaki Sama Da 300
Sai dai ya ce an samu raguwar tikitin da aka sayar da kashi 19 cikin 100 a watan Agusta, saboda an samu Naira miliyan 471 a watan Yuli.
“Fina-finan 37 da aka nuna a watan Agusta sun samu sama da Naira miliyan 378 bayan an kammala tattara su.
“Fina-finan Hollywood 13 sun kai kashi 72.4 yayin da Fina-finan Nollywood 16 suka yi kadan fiye da kashi 22 cikin dari.
Ya ce manyan fina-finai biyar da suka fi samun kudi a watan Agusta su ne: Thur: Love and Thunder, Bullet Train, Beast, Hey you! da League of Surpets.
Ajayi ya ce fina-finan da za su fito a watan Satumba su ne: Inda Crawdads Sing, Passport, Symphony, Inside Life, Finding Ireti, The Woman King, Ticket of Life, Ticket of Paradise, Don’t Worry Darling.
Sauran su ne: Brotherhood, Smile/Tad Ya Lost Explorere da The, Dubi Yadda Suke Gudu, Choke, The Enforcer, Anikulapo da Osorongo.
A wani labarin kuma: Rikicin PDP: Makinde, Fayose, Wike Da Wasu Sun Gana A Ibadan
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya gana da wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP, tare da hasashen matakin da zai dauka na gaba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan ya biyo bayan kuri’ar amincewa da kwamitin zartarwa na kasa ya kada kan amincewa da shugabancin Sanata Iyorchia Ayu.