Kamfanin na Dana Air ya bayar da gudunmawar kayayyaki ga gidajen tsofaffin mutanen a Legas da kuma gidajen marayu da dama a fadin jihar.
Kakakin Kamfanin Dana Air, Kingsley Ezenwa, ya ce tallafin ya yi daidai da tsarin CSR na kamfanin da falsafar tallafawa al’ummomi da kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) wadanda ke da manufofi iri daya.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka ba gidan Marayu na Favid Orphanage, da gidan marayu na V.O.W (Hope) sun hada da buhunan shinkafa, spaghetti, tufafi, Taliya, abubuwan sha, da sauran su.