Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gidan adana kayan tarihi na Horniman da ke Kudu maso Gabashin birnin Landan ya amince da dawo da tagulla 72 da aka wawure a yayin tsohon mulkin Birtaniya da ake kira Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake matsin lamba ga hukumomin Turai kan su mayar da kayayyakin tarihi da aka sace a lokacin mulkin mallaka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Da Nata Kalubalen Kasar Burkina Faso Ta Nemi Shawarar Najeriya Kan Yadda Zata Yaki Ta’addanci
Har ila yau, Hukumar dake kula da gidajen adana kayan tarihi da ta Najeriya, a farkon wannan shekarar, ta nemi a mayar da kayayyakin da aka sace.
“Mallakar abubuwa 72, wadanda aka kwace daga birnin Benin da karfin tsiya, a lokacin da sojojin Birtaniya suka mamaye a watan Fabrairun shekarar 1897, za a mika su ga gwamnatin Najeriya, biyo bayan shawarar da hukumar Horniman ta yanke,” a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon gidan adana kayan tarihin.
Wani bangare na kayayyakin sun hada da allunan tagulla guda 12, da aka fi sani da Benin Bronzes, wani bagadin zakara na tagulla, kayan bikin hauren giwa da tagulla, kararrawar tagulla, da mabudin fadar sarki.
A cewar wata sanarwa da shugabar kwamitin amintattu na gidan adana kayan tarihi, Eve Salomon, ta ce mayar da kayayyakin abu ne da ya dace.
“Honiman ya yi farin cikin samun damar ɗaukar wannan matakin, kuma muna fatan yin aiki tare da NCMM don tabbatar da kulawa na dogon lokaci ga waɗannan kayan tarihi masu daraja,” in ji Salomon.
Ya kara da cewa, “Shaidun sun fito karara cewa an samu wadannan abubuwa ne ta hanyar karfi, kuma tuntuba daga waje sun goyi bayan ra’ayinmu na cewa yana da kyau kuma ya dace a mayar dasu ga mai mallakarsu Najeriya,” in ji shi.
Shugaban hukumar ta NCMM, Farfesa Abba Tijani ya yi maraba da matakin.
Ya ce, “Muna matukar maraba da wannan shawarar da masu kula da gidajen tarihi na Horniman suka dauka. Bayan amincewar da hukumar agajin ta yi, muna sa ran tattaunawa mai inganci kan yarjejeniyar lamuni da hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da gidajen tarihi ta kasa da kuma Horniman.”