• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Sunday, April 2, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Shirye-Shirye Na Musamman

Gidan Solo: Matattarar nishadi ko ta gurbata tarbiyyar matasa?

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
May 24, 2019
in Shirye-Shirye Na Musamman
Reading Time: 6 mins read
25 0
0
34
SHARES
313
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

A shekarun baya, an fi sanin Gidan Solo da sunan Gidan Dirama, wanda wani tsarin nishadantarwa ne dadadde da ake gudanarwa a wasu birane, musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Kamar yadda tsarin yake tun asali, matasa ne maza da mata kan taru, suna gabatar da wasan kwaikwayo na barkwanci da kade-kade da raye-raye, domin nishadantar da mutane. Kuma yawancin ’yan wasan da ke gudanar da tsarin, a nan suke fara haskawa, kafin daga bisani su dawo masana’antar Kannywood domin shirya fina-finan zamani na Hausa.

Binciken Aminiya ya samo bayanin cewa Shu’aibu Idris, wanda aka fi sani da lakanin Lilisco ne ya kirkiri sunan Solo, ko ’Yan Solo a shekarar 1999 a gidan Diramar Tarauni da ke Kano. Daga lokacin nan aka maye gurbin sunan Gidan Dirama da Gidan Solo kuma tun daga lokacin lamarin ya fara tabarbarewa.

A yankin Birnin Tarayya Abuja, binciken Aminiya ya gano cewa akwai akalla gidajen solo guda 40. Kuma akwai akalla guda 25 a yankin Kudu Maso Yamma, domin a garin Ogere na Jihar Legas kawai akwai gidajen solo guda uku. Sannan akwai su a Jihar Kaduna, inda fitaccensu shi ne wanda ake gudanarwa a Cibiyar Adana Kayan Tarihi da ke Unguwar Sarki Kaduna, kafin daga baya suka koma Dandalin Gamji da sauransu.

’Yan mata da zawarawa ne ke hawa dabe da sunan nishadantar da ’yan kallo, inda suke raye-raye da kuma wasan kwaikwayo na barkwanci. ’Yan kallo kuma suna biyan kudi kama daga Naira 50 zuwa sama domin shiga irin wadannan gidaje. Akwai kuma abubuwan da ake sayarwa a wasu gidajen da suka hada da kayan maye.

A tsarin Solo, ana tara mata suna bibiyar wakokin Hausa na zamani, suna rawa. Masu kallo wadanda yawanci maza ne, suna yi musu likin kudi. Amma ba a rawa da likin kudin kadai abin ya tsaya ba. A lokuta da dama Gidan Solon kan kasance matattarar kangararrun mutane maza da mata, inda ake badala iri-iri – abin da wasu suka ce ya saba wa addini da al’adar Malam Bahaushe.

A yayin rawar, maza daga cikin ’yan kallo da dama sukan je ga matan da suke sha’awa su ‘taya.’ Idan sun shirya, ko dai su tafi da su ko kuma su matan su kai su dakinsu, inda a nan yawancin matan sukan koyi shaye-shaye da zinace-zinace da sauransu, kasancewar suna zaman kansu ne kawai a karkashin masu gidansu da ke gudanar da Gidan Solon.

A lokacin da matan suke rawa, a wasu gidajen mai gabatarwa yakan bukaci kowace ta matsa kusa da ’yan kallo ta nemo kudi. Su kuma sai su shiga cikin masu kallon suna musu salon amsar kudi daga hannunsu.

A nan ne a wasu lokutan ake hada yarjejniyar tafiya gida da su ko amsar lambar waya ko kuma shirya inda za a hadu. Wannan ya sa neman mata a gidajen bai da wahala saboda idan har ka je da kudi, da kansu matan za su kawo kansu.

Bincike ya nuna cewa harkar ta bata rayuwar mata da dama, inda suke koyon shaye-shaye domin yawancinsu ba za su iya abin da suke yi ba sai suna cikin maye wato suna jin su a ‘sama.’ A sakamakon zinace-zinace, har ma wasu sukan haifi ’ya’yan rariya, wasu sukan mutu ma a harkar.

Da zarar mace ta sauka a Gidan Solo, ta koma karkashin kulawar mahukunta gidan dari bisa dari, inda za su rika juya ta yadda suka so.

Bincike ya nuna cewa Gidan Solo ya zama matattarar mata da zawarawa da suka guje wa aure watakila saboda sabani da aka samu tsakanin iyayensu a kan auren dole, ko kuma tsakaninsu da mazan da aka aura musu ba sa so. Sannan kuma Aminiya ta gano cewa yawancin mata suna baro garuruwansu ne da sunan aiki ba tare da an san ainihin abin da suke yi ba, domin sun san ba abin kirki suke yi ba kuma a haka suke tara kudade su kai wa iyayensu.

Haka kuma bincikenmu ya nuna mana cewa direbobin tirela suna taimakawa wajen kai mata Gidan Solo, sannan kuma akwai manyan mata da suke zama ejan na kananan matan, inda suke hada su da maza, sannan su kawo musu kudin da suka samu su raba, su kuma suna zama a gidansu.

Dalilin da ya sa matan suka zabi harkar Solo maimakon aure

Aminiya ta samu zantawa da wasu daga cikin ’yan mata da zawarawa da ke zama a gidajen Solo, inda suka bayyana dalilansu na zaba wa kansu irin wannan rayuwa a maimakon aure.

Amina Ibrahim mai shekara 18 ’yar asalin garin Charanchi da ke Jihar Katsina, ta bayyana cewa nishadantar da jama’a ne dalilinta na shiga harkar.

Ta ce ta dalilin wasan take rike kanta da kuma taimaka wa iyayenta kuma ta ce ba ta da nadama. “Nakan samu lokaci in je gida bayan kamar duk wata hudu, in yi kamar kwana biyar tare da iyayena. Sai dai ba su san wannan ce sana’ar da nake yi ke nan a Abuja ba” inji ta.

Ita kuwa A’isha Muhammad ’yar asalin Unguwa Uku Kano, ta ce ta shafe kamar shekara 8 tana rawar Solo kuma a yanzu tana da shekara 22 ne da haihuwa. Ta ce kawarta ce ta jawo ta kuma a yanzu haka ta samu nasarar gina gida baya ga taimakon ’yan uwa da take yi.

Ita kuwa A’isha Abubakar da ta ce ita ’yar Jos ce, ta danganta shiga harkar da matsalar auren dole.

“An yi mini auren farko a Kaduna ina da shekara 15. Ina son mijina yana sona kuma mun haifi ’ya’ya uku tare. Sai uwar rikonsa ta shiga tsakaninmu ta hanyar asiri, kasancewar shi ma mahafiyarsa ta rasu.

“Bayan mun rabu kuma aka hada ni da wanda ba na so, sai na gwammace zuwa nan. Idan na yi wasa aka sallame ni, nakan yi amfani da kudin in rike kaina, a maimakon shiga karuwanci,” inji ta.

Ta kuma kara da cewa ta samu alheri sosai da take tallafa wa rayuwar ’ya’yanta da kuma danginta na wajen mahaifiya.

A Gidan Diramar Apapa da ke Legas, wasu matan da ba su so a ambaci sunansu ba sun bayyana cewa sun gaji da zaman Solo amma Hadiza Mammadou wacce ta zo daga garin Dosou na Jamhuriyar Nijar, ta bayyana cewa yanzu ta fara, domin kuwa akwai riba a harkar.

Wasu ne ke bata masu suna

Sadik Dauda Kankiya shi ne Sakataren wani Gidan Solo da ke garin Deidei a Abuja. Da yake amsa tambayar Aminiya a kan yadda suke samun matan da ke yi musu wasa, cewa ya yi mafi yawan lokuta matan ne ke kawo kansu sai su yi musu rajista. Ya ce bincike domin sanin inda suka fito.

Ya ce sukan fara wasa daga yamma zuwa 12 na dare, ban da lokacin Azumi da suke jinkirta fara wasa zuwa karfe 8 na dare. Ya ce ribarsu ta hada da kudin da suke karba a wajen shig, sai kuma liki da ake yi a lokutan rawa ko gasa, inda suke kasafta kudin a tsakaninsu da mata da samari da makada da sauran ’yan aikin gidan.

Ya ce babbar ribar sana’arsu ita ce sanayyar manyan mutane na nesa da na kusa da ke zuwa gidajen don samun nishadi.

Wani mai gudanar da daya daga cikin wuraren da wakilinmu ya ziyarta a Abuja, Malam Yusuf Usman da aka fi sani da suna Ba-Matsala kuma wanda ke matsayin Ma’ajin kungiyar ta kasa ya ce akwai wasu da ke gudanar da ire-iren gidajen da yawa da ba su yi rajista a karkashinsu ba. Sannan kuma su ne suke bata masu suna kasancewar ba su tsare dokoki da kungiyar ta gindaya ga duk masu sha’awar gudanar da harkar. Ya ce daga cikin dokokinsu akwai hana duk wadda ba ta kai shekara 18 ba, da hana shan miyagun kwayoyi ko shiga da makami kamar yadda aka yi gargadi a jikin wani allo da wakilinmu ya ga an lika a mashigar gidan da yake jagoranta.

Kuma ya ce ba su yarda macen da ke karkashinsu ta bar gidan bayan an tashi wasa da dare don magance matsalar karuwanci, sannan duk wadda aka samu da hakan, akan ci tarar ta idan ta dawo washegari, ko kuma a dauki wani matakin ladabtarwa a kanta kamar kora. Sannan ya ce harkar tasu na samar da tarin abin yi ga mutane da dama.

Akwai bambanci tsakanin Solo da Kannywood

Da Aminiya ta tuntubi fitaccen furodusan fina-finan Kannywood, Nazir Danhajiya, ya bayyana cewa wani lokaci gidan Gala kan samar da jarumai ga Kannywood, yayin da ’yan fim kuma kan je gidan domin su yi wasa su samu kudi idan an gayyace su.

Ya ce, “akwai bambanci sosai tsakanin gidan Gala da kuma Kannywood. A gidan Gala raye-raye da sauran wasan dabe ake yi amma a Kannywood kuma fim ake dauka da kyamara wanda yake kunshe da rubutaccen labari.

“Tabbas a wani lokaci gidan Gala da Kannywood kan taimaki juna, musamman ’yan fim za su je su yi wasa su samu kudi, inda su kuma ’yan Gala akan sa su a fina-finai amma a zahirin gaskiya abubuwa biyu ne mabambanta.”

Previous Post

BUHARI KARO NA BIYU: Muhimman Abubuwan da ya kamata ya fuskanta

Next Post

A’isha Buhari Ta Saka Mata Da Kananan Yara Cikin Bikin Rantsar Da Shugaban Kasa

Next Post

A'isha Buhari Ta Saka Mata Da Kananan Yara Cikin Bikin Rantsar Da Shugaban Kasa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2507 shares
    Share 1003 Tweet 627
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2280 shares
    Share 912 Tweet 570
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2053 shares
    Share 821 Tweet 513
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1766 shares
    Share 706 Tweet 442
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1390 shares
    Share 556 Tweet 348
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

NCC Na Shirin Samar Da Cibiyoyin Neman Taimakon Gaggawa

April 2, 2023
Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

Ukraine Tayi Tir Da Sabon Muƙamin Rasha A Kwamitin Tsaro na MDD

April 2, 2023
Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

Ku Shirya Barin Gidan Gwamnati – ADC ta Fadawa Gwamnan APC

April 1, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
Labarai

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
Labarai

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8
Labarai

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023
Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus

April 2, 2023
Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba

April 2, 2023
Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

April 2, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Yanzu-yanzu: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Yayi Murabus
  • Ganduje Ya Shirya Taron Addu’o’i Ga Sabbin Shugabannin Da Aka Zaba
  • Harin Gidan Yarin Kuje: An Gaza Kamo Fursunoni 460 Tsawon Watanni 8

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In