Gidauniyar Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Hajiya Binta Aminu Bello Masari(Bima Foundation), ta tallafawa mata yan Gudun Hijira da Marayu su 200 da Kayan abinci da kudade.
Kwamishinan Wasanni Da Walwalar Jama’a Na Jihar Katsina Alhaji Sani Aliyu Danlami, shine ya mika tallafin ga wadanda suka amfana a Katsina.
A cewar Kwamishina Danlami, Mata 100 ne suka amfana da buhunan shinkafa kowaccen su, a yayinda wasu su 100 aka basu tallafin Kudi naira dubu goma-goma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasaki dukkannin barayin dake fadin gidan yarin Najeriya, Falana ya caccaki Shugaba Buhari kan Afkuwar da yayi wa Dariye, da Nyame
Wannan tallafi dai abu ne da gidauniyar ta BIMA Ta saba gudanarwa a kowace shekara ga marayu da sauran mabukata domin su san cewa an kula da su.
Alhaji Sani Aliyu Danlami, ya bukaci wadanda suka amfana akan su saka wa karamcin ta hanyar gudanar da addu’oin fatan nasara ga Uwargidan Gwamnan Hajiya Binta Aminu Bello Masari.
Kwamishinan ya yi kira ga masu hannu da shuni akan su rika sadaukar da wani bangare na dukiyar su wurin taimakawa mabukata, musamman a cikin wannan wata na Ramadan.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun yabawa Uwargidan Gwamnan Hajiya Binta Aminu Bello Masari akan kula da ta yi ga rayuwar su.
Sunyi addu’a akan Allah SWT ya saka mata da alkairi, ya kuma yi mata jagoranchi a dukkan lamurransu na rayuwa.