Gidauniyar Kwankwasiyya ta kara jaddada kudirinta na bawa harkar ilimin matasa, da inganta rayuwar zawarawa da marasa karfi fifiko. Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ne ya sanar da hakan ranar Talata yayin bikin bita ga dalibai 242 da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyinsu domin zuwa karatu kasar Indiya da Sudan.
Majiyar mu ta sanar da ita cewa dalibai 234 daga cikin daliban zasu tafi kasar Indiya yayin da 8 zasu tafi kasar Sudan. Abba Kabir Yusuf ya ce wannan shine karo na farko da wata kungiya ko gidauniya a Najeriya ta taba daukan nauyin karatu da yawansu ya kai adadin da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyi.
Ya bukaci daliban da su kasance jakadu nagari ga jihar Kano da Nijeriya a kasashen da zasu je domin yin karatun. Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, ya ce wannan ba shine karo na karshe da gidauniyar Kwankwasiyya za ta dauki nauyin dalibai zuwa kara karatu a kasashen ketare ba, tare da bayyana cewa gidauniyar na cigaba da kokarin ganin yadda za ta fadada aiyukanta na taimakon jama’a.