Abubakar Aliyu Ministan ayyuka da gidaje, yace gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta bada biliyan dari da arba’in da uku ga jahohi biyar don gyaran manyan tituna. Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Ministan ayyuka da gidaje, yayi wannan jawabinne lokacin da ya kai ziyara wajan gwamna Atiku Bagudu a gidan gwamnatin Jahar kebbi.
Abubakar Aliyu Minista kuma kwararren injiniya, wanda yaje jahar Kebbi don ganin yadda ayyukan gyaran manyan tituna ke tafiya.
KARANTA:- Tirkashi: Yan sanda a Kaduna sun cafke mutane 492 tare da kwato shanu 679
“Cikin hanyoyin da muke dasu a wannan kasar, kimanin tsawon kilomita 34,000 ne hanyoyi ke karkashin mallakin gwamnatin tarayya, wanda a halin yanzu ana cigaba da aikin a kan hanyoyi da suka kai tazarar kilomita 13,000, inda sama da ma’aikata 800 ke kan aikinsu.”
“Kamin dai wannan lokacin, gwamnatoci jahohi basa samu damar cigaba da gyaran tituna mallakar gwamnatin tarayya saboda rashin tsaro dake cikin jahar.”
“Gwamnatin tarayya za ta amince dasu gyara tituna mallakar gwamnatin tarayya a jahohin su, sai daga baya ta biyasu abunda suka kashe.”
“A dai tsakanin shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta samar da wani kwamiti (FEC) da yake duba hanyoyi da gwamnatoci jahohi suka gyara.”
“Kwamitin wanda Babatunde Raji Fashola, ya Jagoranta, ya bayyana cewar akwai jahohi ashirin da biyar da suka gyara tituna mallakar gwamnatin tarayya dake Jahar tasu.”
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da baiwa jahohi ashirin da biyar din miliyan dari hudu da saba’in da bakwai su kasafta a tsakanin su.
Gwamna Atiku Bagudu yayi matukar farin ciki ganin Ministan ayyuka da gine-gine, sannan ya yabawa wannan gwamnatin bisa kokarin kafa tarihi na samar da hanyar Sokoto-Tambuwal-Kontagora.
Yace wannan babbar hanya ce, badan hanyar mallakan gwamnatin tarayya ba, sai dai itace babbar hanyar shiga garin Lagos.
“Idan baku manta ba, a shekarar 2015 lokacin da na karbi shugabancin jahar, idan muka gayyaci Sarki Yawuri taro yakan sha wahala, amma yanzu zai zo hankali kwance.
Haka shima Chika-Ladan, yayi kokarin nunawa bakin babbar hanyar Malando-Garin Baka-Ngaski mai tazarar kilomita 45, wanda aka kashe biliyan N2.2 har aka kammala aikin a shekarar 2007.