Gobara ta ƙone Wani Bene a Ilori
Wani Dogon Bene Mai hawa uku a ranar Talata ya ƙone a Ilori, Babban Birnin Jahar Kwara.
Gobarar ta faru ne a Igbala kusa da hanyar Filin Wasa a cikin garin Ilori.
Lamarin a cewar sanarwa daga bakin Mai Magana da Hukumar Kashe Gobara ta Jaha Hassan Hakeem Adekunle ya faru ne da misalin ƙarfe 7:50 a dalilin Wutar Lantarki.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓe akan Zaɓen Ƙananan Hukumomin Katsina
Ya bayyana cewa Motocin Kashe Gobara sun gano cewa an sanya Dutsen Guga a jikin Soket a lokacin aikin ceton.
“Jami’an dake Kula da Kashe Gobara wanda ya Jagoranci Ceton, ya bayyana cewar duk Wutar Lantarki ta haddasa Gobarar, anga Dutse sanye a jikin Soket”, Inji Mai Magana da Yawun.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jahar Kwara Prince Falade John Olumuyiwa, yayi kira ga Mazauna garin dasu jefar da aƙidar barin wani abu a jikin Wuta kafin kwanciya.
Ya bayyana cewa wannan zai taimaka wajen magance Gobara a gidaje, tare da rage Afkuwar hakan.