Gobara ta kone shaguna da dama a babbar kasuwar Kastina-Ala da ke karamar hukumar Kastina-Ala a jihar Benue.
Shaidu sun ce gobarar da ta tashi da misalin karfe 8 na dare a jiya, inda kayayyaki na miliyoyin naira suka lalace.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Sama da shaguna 600 a cewar shaidun gani da ido, gobara ta kone, wanda ya yi sanadin jikkata wasu ‘yan kasuwar da ke kokarin ceto dukiyoyin su.
Shugaban Kastina-Ala, Alfred Atera, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ranar Laraba cewa ya ziyarci wurin da lamarin ya faru kuma ya lura da barnar da wutar ta yi.
Ana shi bangaren Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Engr Donald Ikyaaza ya ce bai da masaniya kan faruwar lamarin.