Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sulaiman Usaini dan shekara daya da mahaifiyarsa mai suna Zainab Yusha’u mai shekaru 25 a duniya a hanyar Gwarzo dake Gidan Kaji a Kano.
Alhaji Saminu Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.
Abdullahi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar jiya Asabar.
“Mun sami kiran waya da misalin karfe 07:00 na safe. daga wani mutum Mai suna Usman Nura kuma nan take muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 07:08 na safe,” inji shi.
Abdullahi ya ce gini ne na bene mai tsayi, da ake amfani da shi a matsayin mazaunin, daki daya ya dan kone yayin da gobarar ta kone falon gaba daya.
Ya ce an mika gawarwakin wadanda abin ya shafa ga mijin matar Mai suna, Malam Usaini.
“Da kyakkyawan kokari na jami’an kashe gobara, mun sami damar shawo kan gobarar domin kada ta bazu zuwa gidan makwabta,” in ji shi.
Sai dai kakakin ya shawarci jama’a da su bi ka’idojin tsaro domin gujewa abubuwan da ba a zata ba, irin wannan lokaci na hunturu.