An tabbatar da mutuwar yara uku a wata gobara da ta tashi a unguwar Rumuchakara, karamar hukumar Obio Akpor ta jihar Ribas.
Daily Post ta ruwiaito cewa, An ce gobarar ta faru ne da karfe 9 na daren ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumomin Abuja Sun Kama Babura 75, Sun Zargi Matuka Babura Da Saba Doka
Yara 5 ne gobarar ta shafa 3 daga cikinsu an tabbatar da mutuwarsu.
Sauran biyun kuma an ce suna karbar magani a Asibiti.
Wasu shaidun gani da ido sun ce mai yiwuwa gobarar ta tashi ne sakamakon hasken kyandir da yaran ke karatu kafin su kwanta barci.
Iyayen wadanda abin ya shafa da aka ce suna cikin dakin nasu a yayin da gobarar ke ci gaba da ruruwa sun samu raunuka yayin da suke kokarin tserewa.
A WANI LABARI KUMA: Kotu Ta Yankewa Masu Damfara Ta Yanar Gizo 66 Hukunci A Ibadan
Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta yankewa wasu masu damfara ta yanar gizo akalla sittin da shida (66) hukuncin dauri daban-daban da gidan yari.
Daily Post ta ruwaito cewa, Hukuncin daurin ya kai daga sati biyu, wata hudu da wata shida na yiwa al’umma hidima zuwa wata goma a gidan yari.