Shaguna da dama a wajen Gadar Apgbo dake Ebute Ero ta Lagos sun ƙone ƙurmus, bayan Gobara ta tashi a Gada da sanyin safiyar ranar Laraba.
Gobarar, wanda ta fara da misalin ƙarfe 1, ta kawo cunkoso a wajen, kuma ta shafi Harkokin Kasuwanci, a yayinda Jami’ai ke ƙoƙari domin magance ta.
Ofishin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa dake Lagos Ibrahim Farinloye yace Ma’aikatar Ayyuka ana kira data kulle hanyar, tare da gudanar da bincike, domin gano lafiyar gadar domin cigaba da amfani da’ita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Kaduna za ta shaida Ɗumbin Ayyukan Cigaba Idan na Zama Gwamna — Cewar Sanata Uba Sani
Yace “Shaguna da dama sun ƙone. Wurin da lamarin ya faru shine Ebutte Ero. Shagunan da suka ƙone yawancin su Kayayyakin Haɗa Biredi da cin cin.
NEMA ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 6:00, an kuma turo Ma’aikatan Hukumomi Kashe Gobara na Ƙasa dana Jaha. Kuma har yanzu ba’a san abunda ya haddasa Gobarar ba.”
Farinloye ya buƙaci masu Motoci dasu yi amfani da wata hanyar.
Yace “zirga-zirga daga hanyar Ikorodu, suyi amfani da Jibowu zuwa Yaba da Onyingbo, daganan zuwa Adeniji zuwa Ebutte Ero ko kuma su cigaba zuwa hanyar Marina.