Wata Gobara ta kone gidan Talabijin na Hi-Impact, gidan talabijin na farko na zamani na HD a Najeriya, dake jihar Ogun.
Gidan talbijin din dai na cikin Babban Fili Amusement Park dake da nisan kilomita 12 da kan babban hanyar Legas zuwa Ibadan, a karamar hukumar Obafemi Owode na jihar Ogun.
Tashar ta kama da wuta ne a jiya Alhamis, inda zauren gabatar da shirye shirye ta, ya kone kurmus.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwalara ta kashe Mutum 146 a jihar Kebbi
Hukumar kashe gobara ta jihar Ogun ta tabbatar da afkuwar lamarin a safiyar yau juma’a, a cikin wata sanar wa da ta fitar.
A cewar sanar war da tasami sahannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara na jihar Bunkunola Kuti, ya ce, wutar ta tashi da karfin gaske, inda batare da bata lokaci ba, jami’an hukumar su ka shanyo kanta .
Kazalika sanar war ta ce” Ma’aikatarn hukumar dake aiki a Ofishin ta na yankin Isheri a jihar Ogun, garkashin jagorancin Kwamandan yankin Engr Akinwade Abiodun ne, su ka kai dauki a gidan talbijin din” a cewar sanar war.
Ya kuma ce, ba’asami rasa Rai ko daya ba, sanadiyar gobarar, sai dai kayayyakin aiki dake dakin gabatar da shirye-shirye tashan sun kone kurmus.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Kwamishinan aiyuka na musamman da kula da harkokin cikin gida na jihar Barista Femi Ogunbanwo, da Daraktan hukumar kashe Gobara na jihar Fatai Adefala, sun ziyarci wurin da lamarin ya afku, domin jajanta wa hukumar gidan talbijin din, da kuma Ma’aikatan ta baki daya a madadin gwamnatin jihar
Comments 1