Wata gobara da ta tashi da tsakar dare Kuma tayi sanadiyar lalata kayyakin miliyoyin nairori a shahararriyar kasuwar sayar da kayayyakin kayan gyaran Mota na Ladipo da ke jihar Legas.
Rahotanni sun nuna cewa, gobarar ta taso ne daga wani shagon hada kayayyakin kayayyakin daki da ke kan titin Ladipo, Mushin, amma daga baya gobarar ta bazu zuwa wani dakin ajiyar kaya inda ake ajiye kayayyakin gyaran Mota kirar Toyota.
Majiyoyi sun ce gobarar da ta tashi sanadiyar wutar lantarki daga shagon na hada kayayyakin daki, daga baya ta kai har zuwa Gini Mai lamba 85 dake kan Titin Ladipo ta hanyar Fatai Atere, na garin Ladipo.
Ko’odinetan Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a yankin Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa gobarar wacce ta shafi wani bene mai hawa uku ta ci gaba da ruruwa har zuwa safiyar yau Litinin.
Farinloye ya ce, katangar tsaron ginin ya haifar da cikas sosai kuma hakan ya hana masu ceto shiga ginin domin gudanar da aiyukan su.
Ya ce ginin da har yanzu yana ci yana haifar da babbar barazana ga lafiyar jama’ar yankin, yana mai cewa gidan ya nuna alamun samun matsala.
Ya ce, “Ginin na dauke da kayayyakin gyara motoci na Toyota iri-iri. An ce gobarar ta tashi ne a wani shago hada kayayyakin daki da ke bayan ginin mai hawa uku. Kuma ana kyautata zaton cewa wutar lantarki ce ta haifar da gorar, da misalin karfe 10:45 na dare ranar Lahadi.”
“Jami’an hukumar NEMA, da na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar da kuma Jami’an ‘Yan Sanda na nan a wajen domin hana barayin wawure dukiyar ‘yan kasuwa.”