Hukumar Kwana-kwana a Jihar Kano ta tabbatar da labarin cewa gobara ta lamushe rayukan wasu mutane biyu yan gida daya.
Kakakin hukumar a Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sabarwa da aka raba wa manema labarai a yau Asabar.
Saminu ya ce gobarar ta auku ne daren jiya juma’a da misalin karfe 10, inda kuma ta kone gidan kurmus ba tare da ta bar ko tsinke ba.
“Wani Mai suna Sabo Wada ya kira mu wuraren karfe 10 yana sanar da mu cewa gobara fa ta tashi a gidan wani Makwancin shi, kuma ta toshe mutane hudu ciki har da yarinya yar shekara hudu.
“To da muka samu wannan labari ne muka gaggauta tura dakarun mu, kuma sun yi nasarar ceto mutane biyu cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai, kuma nan take aka garzaya da su asibitin Mallam Aminu Kano, inda nan ne likitoci suka tabbatar mana da rasuwar su.
Sanarwar ta ce biyu daga mutanen da suka tsallake rijiya da baya sun hada da Fatima Salisu mai kimanin shekara hudu da kuma Saliau Sani dan kimanin shekara 45, yayin da Maryam Sani da yar uwa ce ga mai gidan da kuma Nafisa Abdulkareem mai dakinsa duk sun riga mu gidan gaskiya.
Kawo yanzu babu wani takamaiman Musababbin wannan gobara.