Gobara ta kone wani gida da ke barikin yan sanda na yankin Kwali dake babban birnin tarayya Abuja.
Majiyar yajidar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na daren ranar Talatar data gabata, jim kadan bayan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC ya maido da wutar a yankin.
Wata majiya daga Jami’an Rundunar yan sanda ta ce, “Babu kowa a cikin gidan lokacin da aka maido da wutar lantarki, hayaki ya fara tashi daga wurin, wanda ya ja hankalin dan sandan da ke aiki a kusa da wurin”
Majiyar ta ci gaba da cewa, an sanar da jami’an hukumar kashe gobara kuma sun zo ne bayan an wutar ta gama Kone kayayyakin gidan.
KARANTA WANNAN LABARIN: MAsu Garkuwa da Daliban Bethel Baptist Sun shiga hannu Yan sanda
A nashi bangaren Shugaban yankin Kwali na Babban Birnin Tarayya Abuja Danladi Chiya, ya jajantawa rundunar yan sanda kan afkuwar wannan lamari.
Shugaban yankin ya kuma nemi DPOn yankin, da ya tattara jerin duk wasu kaddarorin da aka samu a sarar su a gidan, don ganin yadda Mahukuntan yankin za sh shiga tsakani.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta tabbatar da samun gobarar, inda ta ce, matsalar wutar lantarki ce ta haddasa lamarin.