Gobara ta kone gidan gwamnan jihar Kano mai barin gado Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya lashe miliyoyin naira kafin kammaluwarsa.
SOLACEBASE ta rawaito cewa gidan da gwamnan zai koma bayan sallama da mulkin, yana kan titin Miagun, bayan Kano Club, a unguwar Nasarawa GRA.
KU KARANTA: Messi Ya Mayar Da Martani Yayin Da Barcelona Ta Soke Kwantiragin Jordi Alba
Gobarar dai ta tashi ne da yammacin ranar Litinin, kuma ta taimaka wajen asarar dukiya mai tarin yawa.
Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar cewa gobarar da ta tashi daga sashin da Dakta Ganduje ke kiwon shanu da sauran dabbobi gaba daya ta lashe bangaren, kuma da yawa daga cikin dabbobin sun mutu a gobarar, tare da konewar wasu kadarori na miliyoyin naira.
Da aka tuntubi Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Abba Anwar, ya shaida cewa ba ya garin, don haka ba shi da masaniyar menene ya faru.
Da yake zantawa da wakilinmu Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, wanda ya tabbatar da barkewar gobarar, ya ce tuni aka shawo kan gobarar a lokacin da ‘yan kwana-kwana suka isa gidan.
A wani labarin kuma: ‘Yan Majalisar Dokokin Bolivia Sun Baiwa Hammata Iska A Zauren Majalisa
Shugabannin kasar Bolivia sun yi Allah-wadai bayan da ‘yan majalisar da ke hamayya da juna suka yi taho-mu-gama a zauren majalisa.
Barkewar rigimar ta samo a saline yayin wata muhawara kan
makomar wani gwamna da ke daure da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin fursunan siyasa.
An yi musayar naushe-naushe na mintuna da dama amma tashe-tashen hankula sun ƙare ba tare da munanan raunuka ba.