Gobara ta kama a fadar babban basarake a jihar Oyo mai riƙe da sarautar Ooni na Ife.
Ana tunanin gobarar ta kama ne a dalilin wutar lantarki da ta zo da ƙarfi. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Cakwakiya: Magidanci ya sheka barzahu bayan matar sa da ya tura kasar waje ta yi ciki
Wani ɓangare na fadar ya kama da wuta ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Juma’a, 28 ga watan Afirilun 2023, jim kaɗan bayan kayan wutar lantarkin fadar sun yi bindiga.
Sai da ƴan kwana-kwana da dogarawan fadar da mutanen gari suka yi da gaske sannann suka samu nasarar kashe gobarar.
Kakakin fadar, Otunba Moses Olafare, ya tabbbatar da cewa tuni har an shawo kan matsalar.
Mummunar Gobara Ta Kone Shaguna 150 A Kasuwar Zariya
A wani labarin na daban kuma, wata mummunar gobara ta laƙume shaguna sama da ɗari da hamsin (150), a wata kasuwa a birnin Zazzau.
A kalla shaguna 150 ne gobara ta kone a kasuwar ‘Yan Katako da ke Sabon Gari, Zariya a Jihar Kaduna.
Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 1 na safiyar ranar Talata, ta ci gaba har zuwa yammacin ranar Laraba.