A kalla mutane biyu ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka sami mummunan raunika, bayan da babban Mota makare da Mai ta tarwatse a garin Ogidi, dake karamar hukumar Idemili ta Arewa, na jihar Anambra.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu, na nuna cewa, motocin bas guda 14 sun kone kurmus, ya yin da kayan milliyoyi suka kone a inda lamarin ya afku, dake kusa da kasuwar saida kayayyakin gini na Kasa da kasa dake garin Ogidi.
Wani shaidan gani da Ido ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da yammacin jiya Lahadi, bayan da motar ta fadi kusa da wani kwalbati.
Wani mazaunin garin Mai suna Uche Michael ya ce, Motar ta na tsaye ne, ya yin da wata tankar ta afkamata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar adawa ta lashe zaben Shugaban kasar Zambia
Ya kara da cewa, ” Nan take motocin Alfarma dake kusa da yankin, suka kama da Wuta, haka ma shaguna da sauran gine-gine su ka kama da wuta suma.” Inji shi.
“Karfin wutar yasa ta gagari jami’an hukumar kashe gobara ta jihar, wurin shanyo kanta” a cewar shi.
Lokacin da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Martin Agbili ya ce, mutane biyu sun mutu, ya yin da akalla motocin bas guda 14, da kuma kayayyakin milliyoyi nairori su ka kone kurmus.
A nashi jawabin, jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Anambra Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, batare da bata lokaci ba, rundunar ta tura jami’an ta, inda lamarin ya afku, domin killace wurin, don kaushewa batagar da amfani da gobarar wurin deban kayan mutane
Comments 1