Gobara ta kone gidaje 10 a lokacin da wata tankar mai dauke da lita 45,000 na fetur ta kama da wuta a Ifo da ke jihar Ogun.
Daiky Trust ta ruwaito cewa, Wata sanarwa da Mista Ibrahim Farinloye, ko’dinetan shiyyar Kudu maso Yamma, na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ya fitar a jiya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safe a kan titin Olambe Matogun, Ifo.
“Ko da yake ba a samu asaran rai ko kuma wani ya samu mummunan rauni ba, Amma kusan gine-gine 10 ne suka kone kurmus a sanadiyar faruwar lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mayakan Boko Haram 70 Sun Nutse A Kogi, Yayin Farmakin Dakarun Soji
“An shawo kan lamarin inda akasarin man fetur din ya zube cikin magudanar ruwa da ke kusa da wurin. Wannan ya ceci al’umma daga mummunan lamari da zai iya shafar mutane da yawa,” in ji Farinloye.
Sai dai jami’in hukumar ta NEMA ya ce kawo yanzu an kashe gobarar .
A WANI LABARIN KUMA: Tinubu Yana Mamakin Dalilin Da Yasa Har Yanzu PDP Take Wanzuwa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana mamakinsa cewa jam’iyyar PDP har yanzu tana nan a matsayin jam’iyyar siyasa.
Ya ce duba da yadda jam’iyyar ta kasance a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar nan, bai iya ganin hanyoyin jiragen kasa da za su iya yin jigilar mutane da dabbobi, da jigilar abinci daga Kudu maso Yamma zuwa Arewa ba.