Dan takarar gwamna a jihar Kaduna na jam’iyyar APC kuma Sanata mai ci Sanata Uba Sani ya yabawa yan kabilar Igbo mazauna jihar.
Sanata Uba Sani ya yabawa al’ummar Igbo mazauna Kaduna ya yi wani taron nuna masa goyan bayansu gare shi da takarar da yake yi.
KARANTA HAKANAN Sanata Uba Sani Ya Dauki Alkawarin Tallafawa Mata Da Matasa Idan Aka Zabe Shi
Uba Sani ya ce gode musu bisa nuna amincewarsu da shi bisa kaunar da suka nuna masa a matsayin dan takarar gwamnan jihar na Kaduna.
Ya ce wannan goyan bayan nasu ya nuna suna son jihar ta sami dorewar samun ayyukan cigaba da kuma hadin kan al’umma.
“Godiya ga al’ummar Igbo mazauna jihar Kaduna bisa nuna kauna da goyon baya ga # DorewarKaduna a 2023” in ji shi.
Duba a kasa akwai wasu hotuna
A Wani Labarin Kuma CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole
Adams Oshiomhole ya zargi babban bankin Kasa CBN da yaudarar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sake fasalin kudin Naira.
A shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya amince da sake fasalin takardar kudin Naira 1,000, da Naira 500, da kuma Naira 200. Matakin, ya haifar da wahalhalu a tsakanin ‘yan Najeriya da ke fafutukar sanya hannu kan sabbin takardun kudi yayin da ranar 10 ga watan Fabrairu ke karatowa. Dangane da rikicin canjin Naira, CBN ya ce ba zai tsawaita wa’adin ba.