- Shahararen ɗan wasan zari-rugar nan wato Odell haji mummunan rauni a dai dai lokacin da ƙungiyarsa take fafata wasa kuma wasan nasu yayi zafi sosai. Ana cikin fafata wasanne aka ga wannan gogaggen ɗan wasan ya kwanata inda yayi nuni da cewar tabbas ya sami rauni.
Daga bisani likitoci sunje wajensa inda suka fara duba lafiyarsa akan yadda aka ga ya kwanta yana neman agaji. Haka zalika daga kwanciyar da yayi wasu ‘yan wasan ƙungiyar tasu suka je wajensa ganin yadda baizaba kwanciya kokuma ya zauna ba idan har yana fafata wasan na zari-ruga.
Amma bayan likitoci sun duba lafiyarsa anan aka gane cewar tabbas yaji mummunan rauni kuma raunin da ka iya sakashi har a gama kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 bazai sake bugawa ba wato zaita yin zaman jinya kenan na wata da watanni.
Shidai wasan zari ruga wasa ne na majiya ƙarfi inda mafi yawan masu fafata shi suna da manyan jiki kuma murɗaɗaɗe inda za a ga yanayinsu ma daban yake. Kuma wasan na zari-ruga wasane da ake yawan turmushe mutane sosai.