Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da mamaye ofishin yakin neman zabenta da ke jihar Gombe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu da ake zargin magoya bayan jam’iyyar APC ne a jihar suka aiwatar da hakan.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja, ranar Litinin.
Ya ce, “Wannan mataki na tsoro da tsokana da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jagoranta na gazawar gwamnatin APC a jihar Gombe, kira ne na kawo karshen zaman lafiya ga daukacin al’ummar jihar, wadanda suke so da burinsu da kudurinsu, shugabanci nagari ya ci gaba da tabbata a jihar.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Tabbatar Da Sace Wani Fasto Tare Da Neman Kudin Fansa
“Jam’iyyar PDP, ba tare da wata tangarda ba, ta bukaci gwamnatin jihar Gombe da ta gaggauta sake gina ofishin yakin neman zaben da aka rusa tare da bayar da hakuri ga al’ummar jihar Gombe.
“Gwamna Inuwa Yahaya yana cikin tsananin tsoron ofishin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na jihar Gombe wanda ya zama cibiyar hada-hadar jama’a a kokarin kwato jiharsu daga halin kuncin da gwamnatin APC ta jefa su a ciki.
Jam’iyyar PDP ta bukaci Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa da ya ba da umarnin gudanar da bincike kan yadda jami’an ‘yan sandan suka yi wa al’ummar jihar Gombe wannan aikin Ta’addanci.
A wani labarin kuma: Gwamna Bagudu Ya Baiwa Hukumar Hisba Naira Milliyan 100
Gwamnatin jihar Kebbi ta bai wa hukumar Hisba naira milliyan dari, domin cigaba da gudanar da ayyukanta na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar nan.
Gwamna Abubakar Bagudu ne ya bayyana hakan, a jiya lahadi wajen bikin cika shekara 20 da kafa hukumar.