Daga Shamsuddeen Sa’eed Da Yusuf Hamisu
Taron ya gudana ne a ranar Lahadi 2 ga watan Agustan 2020 wanda ya zo daidai da 12/12/1441AH a wani dakin taro a cikin garin Katsinan Dikko.
Shi dai wannan taro shi ne kashi na biyu wanda mahukumtan wannan ‘Group’ suka taba shiryawa, inda na farko ya gudana a cikin garin Kaduna a lokacin bikin karamar sallar shekarar da ta gabata.
Wannan taron ya wakana ne karkashin jagorancin shugaban kwamitin shirye-shirye na dandalin wato Halliru Abubakar Dabai. An gabatar da muhimman batutuwa da dama wanda suka hada tarihin kafuwar dandalin tun daga farko har ya zuwa lokacin da ake yanzu sama da shekara 5.
Wanda ya kirkiri dandalin wato Shamsuddeen Sa’eed Mu’az ne ya yi jawabi. A cikin jawaban nasa ya fadi kalubalen da ya fuskanta kafin kafuwar gidan, da kuma nasarorin da gidan ya cimmawa, inda ya ce babbar nasarar da gidan ya cimmawa shi ne kokarin hadakan matasa da kuma sadar da ingantattar alaka tsakanin matasan Nijeriya baki day aba tare da nuna kowanne bambanci ba, wanda karkashin hakan a yanzu ana kokarin kafa kungiya mai zaman kanta ta muryar matasan Nijeriya baki daya wacce za ta maida hankali kan ayyukan ci gaban matasa da taimakon gajiyayyu da marayu da kuma marasa karfi, koyar da sana’o’i dogaro da kai, yaki da shaye-shaye, fyade, da sauran munanan dabi’u, da kuma ankarar da al’umma a duk abin da ya shige masu duhu, kuma ya ce tuni shirye-shiryen sun yi nisa kuma suna samun nasara sosai.
Daga bisani aka rantsar da sabbin shuwagabannin tare da sauke tsaffi sabbin shuwagabannin da ya faro ne daga Chairman din group din Ustaz Yusuf Hamisu har zuwa PRO Halima Abdullahi.
Tun kafuwar group din duk bayan wata 6 ana gudanar da zabe na shugabannin group tun daga Chairman har zuwa PRO mukamai sha biyar. Wanda kuma satika kafin taron aka yi zabe a group din.
A lokacin jawabin tsohon Ciyaman Suraj Salam Shinkafi a madadin tsaffin shuwagabannin da suka sauka, ya fadi nasarori da kuma kalubale da ya fuskanta a lokacin da yake jagorantar dandalin muryar matasan mai dauke da membobi sama da dubu sittin da hudu (64, 000) sannan ya bama Ciyaman mai ci shawarwari masu amfani, daga karshe ya yi fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
Shima Ciyaman mai ci wato Ustaz Yusuf Hamisu a lokacin jawabinsa ya yi farinciki kwarai da gaske kuma ya jinjina ma tsohon shugaban musamman ganin cewa karkashin gwamnatinsa aka shirya gangamin taron kuma ya kawo su jihar sabon Ciyaman wato Katsinan Dikko,
Tare da kafa tushe na bude kungiya mai zaman kanta ta MURYAR MATASAN NIGERIA daga karshe ya yi godiya ga membobin da suka zabe shi ya kuma yi musu alkawrin aiki tukuru a tsawon wa’adin mulkin da zai yi na shekara daya.
Taron dai ya samu halartar membobi da dama daga sassan kasar nan kama daga arewaci har ya zuwa Kudancin kasar, daga karshe an yi addu’oin neman samun zaman lafiya musamman arewacin Nijeriya da ma kasa baki daya.