Tsohon mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona wato Pep Guardiola ya bayyana cewar shida Barcelona a matsayinsa na mai horas wa sai gani sai hange domin ba lallai ne ya sake horas da ƙungiyar ta Barcelona ba.
Hakan ya biyo bayan jita jitar da ake ta yaɗawa dangane da cewar guda daga cikin ‘yan takarar shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Barcelona ya bayyana cewar da zarar ya sami nasarar zamowa shugaban Barcelona to zai sake dawo da tsohon mai horas da ƙungiyar wato Pep Guardiola.
A makon daya gabata ne dai shgaban ƙungiyar ta Barcelona ya sauka wato Josep Maria biyo bayan matsin lamba da yaje fuskanta da kuma suka sosai da sosai daga magoya bayan ƙungiyar.
Guardiola dai ya bayyana cewar idan aka ganshi a filin wasa na Barcelona to yaje kallon wasansu ne kokuma yaje a matsayin mai horas da wata ƙungiyar dazata kara da Barcelona, kokuma idan yaje ganin gida ya wuce ta kusa da filin wasan na Camp Nou.
Guardiola dai ya horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona harna tsawon shekaru huɗu wato daga shekarar 2008 zuwa 2012. Yayimusu bajinta sosai inda ya lashe kofuna da dama daga ciki harda gasar zakarun nahiyar turai guda biyu.