Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sunayen mutum 5,351 cikin mutane 41,971 da suka cike fom na neman aiki da gwamnatin jihar ta fitar akan yanar gizo.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Malam Nasir El-Rufa’i kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adeleke ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
Tuni dai aka fitar da sunayen mutum 13,700 cikin mutum 41,971 da suka cike fom, kuma aka yi musu gwajin mataki na farko, inda aka yi tankade da rairaya aka kuma samu adadin mutum 5,351 da suka shallake gwajin na farko na jarrabawar da aka gabatar akan na’ura mai kwakwalwa.
An dai gabatar da wannan jarabawar gwaji ne ga wadanda suka cancanta a makon da ya gabata, tsakanin 7 zuwa 13 ga watan Oktoba da muke ciki.
Za a kuma fara tantance wadannan mutum 5,351 da aka fitar da sunayensu a wannan mako, wanda hakan shi ne zai zama karo na farko da mutanen za su fara ganawa da wakilan gwamnatin jihar Kaduna bayan da a baya suka yi ta mu’amala da na’ura wajen cike fom.
Mutanen da suka tsallake gwajin farko za su samu sakon rana da wajen da za a tantance su ta hanyar sakon Imel.