Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a a Maiduguri, ya mika gidaje 81 masu dakuna uku tare da cakin jimlar kudi Naira miliyan 79m ga likitoci 81 masu neman kwarewa.
An bai wa kowanne daga cikin likitocin wani fili da aka gina rabinsa da gidaje na musamman guda 13 masu beni mai hawa biyu tare da kowane rukunin gidaje shida, inda kuma rabinsa aka shuka fure da kuma tanadar da wuraren wasanni a filin wajen.
KARANTA WANNAN LABARIN; https://dimokuradiyya.com.ng/tinubu-ya-yi-biris-da-ni-bayan-na-janyewa-osinbajo-a-zaben-fidda-gwani-dan-takara/
Bangarorin 13 da ke rukunin sun hada da gidaje 78 yayin da wani ginin bene da ke asibitin tunawa da Muhammadu Shuwa yana da karin gidaje uku, wanda ya samar da adadin gidaje 81.
Biyu daga cikin filaye 81 an kammala su yayin da 79 ba a kai ga kammala su ba.
Zulum ya gabatar da cekin kudin da ya kai Naira miliyan 1m a matsayin tallafin kayan aiki ga likitoci 79 da aka ware musu gidaje 79 da ba su da kayan aiki.
Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar gidajen 81 shine Dr Bulama Gaidam, wanda a halin yanzu ke hannun kungiyar ta’addanci ta ISWAP.
An sace Gaidam ne a ranar Laraba, 16 ga watan Maris, 2022 a Gubio, inda yake aiki a matsayin babban jami’in kula da lafiya na babban asibitin.
Gwamna Zulum ya mika makullan daya daga cikin gidaje biyu da aka kammala.
Da yake magana da matar likitan da aka sace, Zulum ya jajanta mata tare da karfafa mata gwiwa fatan wata rana zata sake haduwa da mijinta.
Gwamnan ya bada tabbacin duk likitocin 81 da suka amfana da cewa gwamnati za ta yi kokarin tallafa musu wajen samar da injin janareta da za a sanya wa rukunin gidajen dan samar da hasken wuta.
Sai dai ya bukaci likitocin da su kafa wata kungiya da za su iya ba da gudummawa ta hanyar nemo hanyoyin da za a ci gaba da kula da gidajen, da kuma inganta tsaron jama’arsu.
Zulum ya yi alkawarin cewa, za a tallafa wa karin likitocin da ba sa cikin mutane 81 da suka ci gajiyar tallafin ta wasu hanyoyi a ci gaba da kokarin gwamnati na inganta jin dadin likitocin don samar da ingantacciyar hidima da ceto da inganta rayuwar bil’adama.
Idan dai za a iya tunawa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya kaddamar da rukunin gidajen likitocin a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, inda bayan haka aka tsara yadda za a gudanar da zaben tuntubar juna da raba wa likitocin da za su amfana.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito A halin da ake ciki, a lokacin da yake mika gidaje 81 da duba lafiyar likitocin, Gwamna Zulum ya bayar da umarnin a samar da motocin bas guda biyu wadanda za su rika tsayawa na dindindin a rukunin domin kai su asibitoci domin kula da lafiya.
A tasu godiyar, wakilin likitocin ya yi alkawarin cewa za su mayar da martani ta hanyar inganta ayyukan jinya ga marasa lafiya a asibitocin su.
Zulum ya kuma zarce zuwa unguwar Wulari da ke cikin birnin Maiduguri inda ya kaddamar da sabbin hanyoyin garin da aka gina da kuma cibiyar kula da lafiya a matakin farko da gwamnatinsa ta aiwatar.