
Gwamanan Jihar Neja Sani Bello ya kaddamar da wani katafaren Asibiti da aka Gina a Kontagora
Gwamana Abubakar Sani ya kaddamar da babban Asibiti na mata da aka Gina a Kontagora daga cikin yunkurinsa na kawo cigaban kiwon Lafiya a Jahar.
Dr. Amina Abubakar Sani matar gwamanan Jihar Neja tare da hadin guiwar Mainstream Foundation suka Gina wani katafaren Asibiti na zamani cike da kayan aiki.
KARANTA:- Matsalar tsaro ya kawo cikas ga karatun Mata a Arewa
Asibitin dai zai bada kulawa ga Mata masu ciwon yoyon fitsari wanda a sana diyyar dadewa wajan nakuda sannan Asibitin zai cigaba da koyarda Mata hanyoyin Kare kansu daga kamuwa da nau’ikan cututtuka daban daban na zamani.
Gwamanan a yayinda yake kaddamar da aikin yayi Kira ga sauran kungiyoyi dazu cigaba da irin wannan aikin don taimaka wajan sauke nauyin dake kan gwamanti.
Gwamanan yayi kiraga ga Matan aure dasu cigaba da ziyartar Asibitin dazaran sun Sami juna biyu don duba lafiyar su.
Gwamanan yace zaiyi kokari wajan tallafawa dukkanin wasu awwuka wadanda kungiyoyin jikai keyi.
Dr. Amina matar gwamana tace kudirin an farasa ne tun shekarar 2019 kuma zai cigaba don tallafawa al’umma.
Daga cikin manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da Fati Lami Abubakar, Karkin Kagara, Alh. Ahmed Garba, Attahiru II, da Sarkin Kontagora, wanda ya turo wakilinsa Engr. Shehu Galadima, Galadiman Kontagora duk sun halarci taron.